Da gaske an harbe ɗan Idriss Deby?

Kafofin yaɗa labarai na Chadi sun ba da rahotanni masu karo da juna game da zargin harbe-harbe a fadar shugaban kasar Chadi a N’Djamena kan wata taƙaddama tsakanin iyalin marigayi Idriss Déby game da naɗin ɗansa Mahamat Idriss Déby Itno a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa.

A wasu jerin saƙwanni daga shafin Twitter na kafar Tchadinfos ta ambato majiyoyi da dama da ba ta bayyana suna ba musanta cewa an yi harbe-harben.

Amma a nata ɓangaren kafar Toubou ta ambato majiyoyin tsaro da ke cewa Mahamat ya ji rauni a harbe-harben sakamakon saɓanin da aka samu.

Tchadifos ta ce “Shugaban riƙon kwarya yana raye kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Babu wani harbi da aka yi kuma babu wani saɓani tsakanin Mahamat da ɗan uwansa Zakaria.”

Marigayi Déby yana da ƴaƴa da yawa, ya yi aure da yawa, kuma yana da yara da ba a san yawansu ba.

A nata labarin kuma Jaridar Alwahida Info mai goyon bayan gwamnati ta ce an ji ƙarar harbin bindiga a Ati, da ke nisan kilomita 378 da gabashin N’Djamena bayan fursunoni sun yi ƙoƙarin tserewa .

Amma Jaridar ta ce “ƙura ta lafa” bayan tura sojojin a yankin.

Daga: Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *