Labarai

Dalilin da ya sa na amince da sabbin takardun Naira –Buhari

Spread the love

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan dalilin amincewar sa ga CBN na sake fasalin takardun kudi na N200, N500 da N1000.

Buhari  ya kuma bayyana jin dadinsa da yadda hukumar buga ma’adanai ta Najeriya (NSPM) Plc ta samar da kudaden da aka sake fasalin.
Buhari ya yi magana ne a wajen kaddamar da sabbin takardun kudi da aka yi gabanin taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba a Abuja.

A cewar shugaban, sabbin takardun kudin Naira an yi musu katangar tsaro da ke da wuyar yin jabu.

Ya kara da cewa sabbin takardun kudi za su taimaka wa CBN wajen tsarawa da aiwatar da ingantattun manufofin kudi, da kuma kara wa dandali na tarihi a Najeriya baki daya.

Hakazalika ya gode wa Manajan Darakta, Daraktoci da ma’aikatan NSPM PLC “saboda yin aiki tukuru tare da babban bankin don ganin an sake fasalin kudin, da kuma buga sabbin takardun Naira a cikin kankanin lokaci.”

Buhari ya ce: “Sake fasalin takardun kudi gabaɗaya yana nufin cimma takamaiman manufofi, ciki har da inganta tsaro na takardun.

“Haka kuma an yi niyyar rage jabunsu, da adana kayayyakin tarihi na kasa baki daya, da sarrafa kudaden da ke zagawa, da rage tsadar kudaden da ake kashewa.

‘’Kamar yadda aka sani, dokokinmu na cikin gida, musamman dokar Babban Bankin Nijeriya ta shekarar 2007, ta bai wa CBN ikon fitowa da sake fasalin Naira.

‘’A bisa wannan karfin, Gwamnan bankin ya tuntube ni a farkon wannan shekarar domin neman izinina na fara aikin sake fasalin kudin.

“Na yi la’akari da duk hujjoji da dalilan da Babban Bankin ya gabatar a gabana.”

Don haka Buhari ya bayyana fatan sabbin takardun kudi za su magance bukatar gaggawa na kula da kudaden da ke yawo.

Ya ce hakan zai kuma magance matsalar tabarbarewar kudaden banki na Naira a wajen tsarin banki da kuma dakile matsalar karancin takardun kudi masu tsafta da ke yaduwa.

Buhari ya kara da cewa takardun da aka yi wa gyaran fuska za su kuma magance karuwar jabun takardun kudi na Naira.

A nasa jawabin, Emefiele ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da ya bayar na sake fasalin da kuma raba sabbin takardun kudi.

A cewarsa, sabbin takardun za su shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, da samar da manufofi masu inganci, tabbatar da hada-hadar kudi da yaki da cin hanci da rashawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button