Dalilin da yasa Buhari bai halarci jana’izar Attahiru ba, daga fadar shugaban kasa

Sojoji sun bude rajistar ta’aziyya ga COAS, wasu a Kaduna

Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari bai halarci jana’izar Babban Hafsan Sojojin (COAS) ba, Laftana-Janar. Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshin soja 10 da suka mutu a wani hatsarin jirgin sama a Kaduna.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu,  yayi magana a shirin Arise TV da aka haska a Legas, ya yi ishara da cewa Shugaban kasar ba ya son “wannan tunanin na rufe hanyoyi, jami’an tsaro suna cin zarafin mutane a kan hanya” duk lokacin da ya fita halartan taro a wajen Aso Rock.

Ya ce: “Ni kaina ina Turai ina wani aiki kuma ban yi magana da Shugaban kasa kan wannan lamarin ba. Amma bari na baku misali guda daya. Shugaban kasar wani mutum ne wanda yake matukar damuwa da kare lafiyar talakawan Najeriya akan tituna.

“Shin kun san dalilin da yasa yanzu yake Sallar Juma’arsa a gidan Gwamnati kuma baya zuwa Masallacin Kasa? Saboda ba ya son wannan tunanin na rufe hanyoyi, mazajen tsaro suna cin zarafin mutane a kan hanya don Shugaban kasa ya samu hanya.

Daga Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *