Dalilin daya sa Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman daga aiki.

Ba sabon labari ne game da dakatarwar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari yayi wa shugabar kula da tashoshin jiragen ruwa na Najeriya ba, wato Hadiza Bala Usman.


Idan za’a iya tunawa, mataimaki ga shugaban ƙasa na musamman akan kafafen watsa labarai, Malam Garba Shehu, shine ya sanar da dakatarwar a shafinsa na Twitter, a daren Alhamis ɗin daya gabata.


Inda sanarwar tace, an naɗa babban daraktan kuɗi, da gudanarwa na hukumar watau Muhammad Bello Koko a matsayin sabon muƙaddashin hukumar.

To sai dai mutane da yawa suna ta mamaki da tunanin ko menene dalili ko hujjar cire wannan ƴar tahalika daga aiki, duba da yadda ba’a daɗe ba da shugaba Muhammadu Buhari ya amincewa Hadiza ta cigaba da jagorantar hukumar a karo na biyu.


Kamar yadda rahoto yake nuni daga ma’aikatar sufuri ta ƙasa, wanda Freedom Radio Kano ta ruwaito, ya nuna cewa akwai saɓani da rashin jituwa da yayi tsamari a yan kwanakin nan tsakanin ministan sufuri na ƙasa Rotimi Amaechi da ita Hadiza Bala Usman.


Majiyar da Freedom Radio ta samu, ya nuna cewa, saboda irin wannan sa-to-ka-sa-katsin ne yasa Rotimi Amaechi zaiyi cikkaken bayani akan dakatarwar da akayi wa tsohuwar shugabar hukumar.

Tun a shekarar 2016 ne dai aka naɗa Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar hukumar, bayan an sauke Habib Abdullahi daga muƙamin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *