
A wata takarda da Jaridar Mikiya ta samu Mai dauke da sa hannun majalisar Malaman ta Kano sun bada sanarwar sauke shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil daga mukaminsa, a cewarsu ya afkar da kingiyar cikin siyasa Lamarin da ya kawo ci baya a garemu

Har’ila yau Malaman sun zargin Sheikh Khalil da yin fada Gwamnatocin da Suka gabata inda suka Malamin yayi fada da Gwamnatin Shekarau yayi fada da Gwamnatin kwankwaso yayi Yanzu Kuma Yana fada da Gwamnatin jihar Kano karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Khadimoul Islam. Kamar yadda sanarwa ta nuna a jikin takardar sunce Shiga Siyasar da malamin yayi tasa Basu Samun komai daga hannun Gwamnati.
A saboda haka, Malaman suka bayar da sanarwar nada Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano.
