Dan Allah Ku saki daliban Jami’ar Greenfield, Shugaba Buhari ya roki ‘yan ta’adda.

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya sha suka a shafukan sada zumunta saboda rokon barayi da su saki daliban da aka sace na jami’ar Greenfield, biyar kuma an riga an kashe su.

Buhari yayin da yake mayar da martani game da sakin dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, ya ce, “Ina sake yin kira da ‘yan ta’addan da su saki daliban Jami’ar Greenfield da duk sauran‘ yan kasa da ke tsare.

“Ba za mu bar wani kalubale ba don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna zaune a cikin kasar inda kowa zai iya motsawa inda ya keso kuma lokacin da yake so-ba tare da tsoron satar mutane daga’ yan fashin ba.”

Amma mutane da yawa a shafin Twitter sun yi mamakin dalilin da ya sa Shugaban kasa zai yi kira ga ‘yan fashin da ya kamata a kama su a kuma hukunta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *