Daya daga cikin dalibin Jami’ar Greenfield wanda aka binne ana kuka da hawaye


An binne Sadiq Sanga Yusuf, daya daga cikin daliban uku na Jami’ar Greenfield, Kaduna da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka kashe a yayin da’ yan uwa da abokan arziki suka yi ta kuka da hawaye.

SaharaReporters ta tattaro cewa Sadiq da ne ga Malam Yusuf Mu’azu, Darakta a Ma’aikatar Ayyuka na Kaduna.

An binne shi tare da ta’aziyar ga mahaifin, wanda kuma ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Jemaa a jihar Kaduna.

An tsinci gawar Sadiq, tare da na Dorathy Yohanna da kuma Precious Nwakacha a ranar Juma’a a kauyen Kwanan Bature, wani wuri da ba shi da nisa da harabar makarantar.

‘Yan fashin sun nemi a ba su Naira miliyan dari takwas

Kaduna na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar sace-sacen mutane ta hanyar ‘yan fashi.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *