Dino malaye yayi Barazanar maka wata Budurwa gaban kotu bisa zargin Bata Masa suna.

Kakakin Majalisar Yakin Neman Zaben Shugabancin Jam’iyyar PDP Dino Melaye, ya yi barazanar shigar da kara a kan wata mawallafiyar yanar gizo, Gistlover, wacce ta alakanta shi da wasu ’yan Najeriya guda biyu, Ashmusy da Nons Miraj.
Mawallafiyar a shafinta na Instagram a ranar Talata ta raba hotunan Ashmusy, Dino Melaye da Nons Miraj a ranar Talata kuma ta yi taken, “I like fine fine pictures sha. Aiki a karkashin Dino ba karamin aiki bane oo. Ina zuwa koma.”
“I like fine fine pictures sha. Hard work under Dino no be small work oo. I dey come.”
Melaye, wanda ya sake wallafa hoton Gistlover a shafinsa na Instagram a yau ranar Laraba, ya caccaki mawallafiyar ya kuma yi barazanar kai kara kan labarin.
Ya ce, “Zan kai kara kotu a wannan karon. Za a same ku. Ban san ko ɗaya daga cikin waɗannan matan ba. Wakilan APC. Ba za ku rabu da karya da labari mara tushe ba a wannan lokacin. Kun dai buga lambar da bata dace ba. ki bayarda hakuri cikin sa’o’i 24 ko kuma a fuskanci sakamako.”
Credit: Instagram | Dino Melaye