Dole ne a rage farashin siminti- Majalisar Dattijai

Majalisar Dattijai ta Najeriya tasha alwashin cewar, duk yadda za’ai dole ne a rage farashin siminti a ƙasar nan.

Wannan al’amari na zuwa ne, yayin da farashin siminti yayi mugun tashin gwauron zaɓi farat ɗaya, inda talakawa ke zargin cewa, kamfanunnikan nayin haka ne da gangan, domin su gallaza masu.


Saboda haka ne, majalisar a matsayinsu na wakilan al’umma, suka yanke shawarar samar da wani kudiri da zai taimaka wajen raguwar farashin na siminti.


Ashiru Oyetola, ɗan majalisa ne, kuma shine ya fara gabatar da kudirin yayin zaman majalisar.
Yanzu dai abin jira a gani yadda wannan kudiri zai samu nasara, duba da yadda mutane ke korafi sosai akan farashin siminti.

Rahoto: Abubakar Mustapha kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *