Labarai

Dole ne muyi anfani da addini domin inganta rayuwar Al’umma ~Cewar Pastor Yemi Osinbanjo.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce dole ne a yi amfani da addini wajen taimaka wa ‘yan kasa don samun ingantacciyar rayuwa.

Osinbajo, a cewar sa a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Laolu Akande, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata a fadar shugaban kasa da ke Abuja da yammacin ranar Asabar, yayin da yake karbar babban Khalifa na Darikar Tijjaniya a fadin duniya, Sheikh Muhammadu Mahi Ibrahim Niass na kasar Senegal.

Ya ce, “Akwai al’ummai da yawa na duniya da suka amfana da tasirin addini a zuciya da kuma sassan jikin bil’adama

“Don haka, dole ne mu yi amfani da addini a kasashenmu (a Afirka) don taimaka wa mutanenmu don samun ingantacciyar rayuwa saboda, a wasu sassan duniya, shugabannin bangaskiya sun yi amfani da addini don inganta rayuwar mutane.”

Ya kuma jaddada bukatar shugabannin addini su rika kutsawa cikin wannan manufa ta hanyar amfani da addini wajen magance kalubalen da ke kunno kai a cikin al’umma.

“Komai halin da ake ciki, mu a Afirka, dole ne mu zauna tare mu tattauna. Kada mu ƙyale yanayin rabuwar Kai da zai hanamu iya zama tare.

“Tare da abubuwan da ke faruwa a fadin duniya, masu imani dole ne su ci gaba da jaddada cewa duka manyan addinai (Musulunci da Kiristanci) suna inganta zaman lafiya kuma dole ne mu bar mutanenmu su yi duk wani addini da suke so.”

Ya yabawa shugaban kungiyar tare da yabawa kungiyar Tijjaniya bisa manufofin ci gaba da kuma tausayawa bukatun al’umma.

Ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin koyi da ke daukar mutane masu bambancin addini.

“Shugaba Buhari musulmi ne mai kishin kasa kuma ni Fasto ne, dukkan mu biyu mun yi aiki tare kusan shekaru 7, ba mu samu matsala ba,” in ji Osinbajo.

Sheikh Niass, wanda ya yi magana da Faransanci tare da fassara ta hanyar mai magana da yawunsa an ruwaito ya gode wa Osinbajo bisa damar da ya samu na ganawa da shi da tawagarsa.

“Mataimakin shugaban kasa mutum ne mai girma da ke da hali na musamman, yana tsaye da kafafu biyu: daya a matsayin shugaban siyasa ya damu da ci gaban al’ummarsa na biyu kuma a matsayinsa na bawan Allah.

“Afirka tana buƙatar mutumin da ya dace da yanayin ka mai ƙwaƙƙwaran ilimin addini da siyasa. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka ka Ya kuma ba ku damar cimma burinku domin kamar yadda na ce, ba Najeriya kadai ba, Afirka za ta amfana da halayenku na jagoranci.”

Ya godewa Buhari bisa goyon bayan da yake baiwa kungiyar, inda ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya, kuma Nijeriya ta shawo kan kalubalen da take fuskanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button