
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu kira ga Najeriya da ta rabu kan suyi wani tunani, ya kara da cewa idan aka raba Najeriya tofa Lallai su sani dole ne sai kowa yayi biza domin tafiya wurare kamar Kano.
Osinbajo ya fadi hakan ne lokacin da yake gabatar da jawabinsa kusan a taron tattaunawa na Bola Tinubu karo na 12 da aka gudanar a bikin tunawa da ranar haihuwar Tinubu na 69 a Kano.
Mataimakin shugaban kasar, wanda shine babban bako na musamman, ya ce shirin farko shi ne a gudanar da taron kwata-kwata amma Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ba da damar daukar nauyin taron wanda zai gudana tare da wanda ake yi a Zoom.
Ga masu son ballewa zuwa kananan abubuwa, zuwa kananan kasashe, watakila ya kamata a tuna musu cewa da ba za mu iya karbar tayin Gwamna Ganduje na zuwa Kano a takaitaccen sanarwa ba tunda duk za mu bukaci biza don zuwa Kano , ”In ji Osinbajo.
Osinbajo ya kara da cewa Kano waje ne mai matukar muhimmanci domin nan ne gidan masu akida da ci gaba.