
Shahararran marubucin Hausa a shafukan sada zumuntar zamani Rabi’u Biyora ya bukaci Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar ganduje da ya mika masa daya daga cikin kujerun kwamishina domin cike gurbin wa’yanda suka yi murabus a kokarin su na tsayawa takara a matakai daban-daban
Biyora ya rubuta Hakane Jim kadan bayan da wasu kwamishinonin Ganduje sukayi murabus ya Kuma rubuta wannan batu ne a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa…
DAN TAKARAR CIKE GURBI…..
Don Allah Baba Ganduje ka bani daya daga cikin kujerun Kwamishinonin da suka ajiye aiki, Baba Ganduje wallahi ni cikekken Masoyinka ne, tun a shekarar 2011 nake tare dakai, kuma zanyi aiki sosai a ragowar shekara dayan data rage…..
Ku tayani addu’ar samun kujerar Kwamishina a Kano.
Matasa masu bibiyar shafin marubucin sun nuna goyon bayan su ga wannan kudri na Rabi’u Biyora.