Duk wa’yanda Suka yi wa gaduje butulci A Yanzu suna Cikin ladama ~Inji Garba Shehu.

Alhaji Garba Shehu, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka yiwa gwamnan jihar Kano tawaye a yanzu haka suna cike da nadama.
Da yake jawabi a wajen bude taron shekarar 2021 na kungiyar Editocin Najeriya a ranar Litinin a Kano, Shehu ya ce jihar ta samu dimbin ci gaba, alkawura, da sulhu a karkashin jagorancin Ganduje.

“Ya kamata mutane su zo su koya daga Jihar Kano,’ ’in ji Shehu.
Ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na bukatar a basu kwarin gwiwa cewa gwamnatoci a dukkan matakai na aiki kai tsaye don kawo karshen rashin tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shehu ya yi kira ga editoci a wurin taron da su ci gaba da inganta zaman lafiya da hadin kai ta hanyar rahotonsu na kafafen yada labarai.

Ya kuma kalubalanci editocin da su yi amfani da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen dinke barakar da ke tsakanin gwamnati da jama’a, musamman ta fuskar yada labarai.

“Ina ganin lokaci ya yi da za mu sa ido a ciki mu ga yadda za mu dakatar da yada labaran karya, sakaci da jita-jita.

“Ina ganin ya kamata mu ma mu yi amfani da wannan damar don tunatar da kawunanmu nauyin da ke kanmu na inganta kan ayyukan yada labarai.

Rokon da zan yi wa abokan aiki na a nan shi ne, bari mu kara ganin kasar da madubin Gaskiya a maimakon madubin da yake na karya” in ji Shehu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *