
Da sanyin safiyar jiya asabar ne ma’aikatan asibitin koyarwa na Asibitin Malam Aminu Kano suka tashi da wani abun taajibi sakamakon cin karo da suka yi da wani jariri an yasar dashi a gefen kwata, cikin tsumman zani ba tare da kowa a wajen ba.
Biyo bayan faruwar wannan lamari, zargi yayi ƙarfi cewar wata kila an yasar da jaririn ne cikin dare saboda cikin shege ne, kuma bata so a kamata.

Hakan ne zuwa ne yayin da wasu suke kashe maɗuɗan kuɗaɗe don ganin Allah ya albarkace su da ƴaƴa, sai gashi wasu kuma sun samu har suna yarwa.

Allah ya tsare mu da yin aikin dana sani.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru