EFCC ta cafke wasu mutane 57 da ake zargi da zamba ta intanet, tare da kwato bindigogi biyu.

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC, Ofishin shiyya na Ibadan a ranar Juma’a, 12 ga Maris, 2021 ta kama mutane hamsin da bakwai da ake zargi da zamba ta hanyar intanet a maboyar otal dinsu kuma sun kwato bindigogi biyu na fanfo.

An cafke wadanda ake zargin ne a Yewa Frontier Hotel & Resort, Ellysam Hotel & Suits, Afrilu Suits da IBD International Hotels, duk a Ilaro, Jihar Ogun.

Wannan aiki ya biyo bayan bayanan sirri ne da ke alakanta su da ayyukan yaudara, wanda ya samo asali daga damfara ta soyayya a shafukan sada zumunta da dama, da samun kudi ta hanyar yin karya da sauran hanyoyin intanet.

An kwato motoci na musamman guda hudu, wayoyin hannu, kwamfutar tafi-da-gidanka, bindigogi biyu da takardu da dama daga wadanda ake zargin.

Wadanda ake zargin sun hada da: Olatunji Opeyemi, Akintunde Michael Oluwashola, Babatunde Gbolahan, Emmanuel Oluwadamliare, Ogundare Adewunmi, Popoola Salmon, Adebayo Toheed Olamilekan, Bakare Kudus, Michael Moyosoro, Olatunji Tosin, Ishola Wasiu, Ugwu Ekenedelichukwu David, Salaud Fatai Abiodun, Idowu Adeola, Oladipupo Nurudeen, Olasoju Mohammed, Onipede Toheed, Bello Abdullahi, Olatunji Abiola, Ogunbayo Peter, Adeyemi Abraham Ismail, Toheed Oluwaseun, Abiola Mutiu, Shoneye Idowu, Badmus Farouk kayode, Ilyas Abubakri Olanrewaju, Oladeji Basiola Soliu Adewole.

Sauran sune: Odewunmi Samuel Pelumi, Oyeniyi Telslim Olashile, Shogbamu Olatunbosun Lukeman, Adebanji Timilehin Michael, Bangbose Jonathan Olakunle, Ashore Damilare Godwin, Bello Tobiloba Abdullahi, Ogundeji Babaji Ibrahim, Bashir Ayodeji Toheed, Olaleye Biola Farudeen, Sunday Osunaiki Emmanuelole , Babajide Oluwapelumi Bolaji, Oluyide Ridwan Olawale, Abdullahi Umar Farouq, Opeloyeru Kehinde Abdulwaheed, Adeola Olusegun Israel, Shittu Ganiyu Olamilekan, Abdullahi Narudeen Owolabi, Ganiyu Kudus Olawale, Biodun Okeowo Sunday, Aiyemidotun Moses Omolade, Alade Hammed Oluwatosde Ola, Gbenga Akanbi, Awobaju Koyinsola Damilare da Bello Uthman Olayithan.

Za a gurfanar da su a kotu da zaran an kammala bincike.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *