Labarai

EFCC ta gurfanar da ƙanin ​​Gwamna Yahaya Bello da wasu mutane biyu a gaban kuliya bisa zargin almundahanar N10bn

Spread the love

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da wani Aliyu, wanda aka ce kani ne ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

A wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Alhamis, ta ce an gurfanar da Aliyu tare da wani Dauda Suleiman a gaban mai shari’a James Omotosho, bisa tuhume-tuhume 10 na almundahana da kuma karkatar da kudade.

Uwujaren ya bayyana cewa Aliyu da Suleiman tare da wani mai karbar kudi a gidan gwamnati, Abdulsalami Hudu, sun cire naira biliyan 10.2 daga asusun jihar domin amfanin kansu.

Wadanda ake tuhumar dai sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su, yayin da aka dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button