EFCC ta kama wasu ‘yan damfara masu amfani da yanar gizo gizo har guda biyar a Kano.

Ofishin shiyyar Kano na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati da Tattalin Arziki, EFCC, ya tabbatar da nasarar cafke wasu mutane biyar da ake zargi da damfara ta yanar gizo gizo a jihar.

A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta bayyana wadanda ake zargin a matsayin Abdulaziz Shamsuddeen Umar, Adamu Sufiyan, Abdulsamad Abdulaziz, Mustapha Musa, da kuma Suleiman Alexander Adeiza.

Sanarwar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a Danbare Quarter, daura da Jami’ar Bayero, Kano sakamakon bayanan sirri da suka samu kan damfarar da ke da alaka da yanar gizo.

Za a gurfanar da su a gaban kotu idan an kammala bincike.

Akwana kwanan nan hukumar EFCC ta matsa da kai farmaki wajen miyagu masu harkar ta’annati da damfara ta kuɗi, domin ko a ranar Alhamis din da ta gabata, hukumar ta EFCC ta cafke wani dan wasan barkwanci na kafar sada zumunta ta Instagram da kuma kafar yada labarai ta yanar gizo, mai suna Nwagbo Oliver Chidera, wanda aka fi sani da Pankeeroy da wasu ƙarin mutum 34 saboda zarginsu da hannu a zamba da ke da alaƙa da kwamfuta a Legas.
An gano wasu samfurin Mercedes Benz AMG GLE mai daraja N36,000,000 (Naira Miliyan Talatin da shida) a wajen waɗanda ake zargin, kuma sun ce sun shiga badaƙalar bitcoin ne bayan sun kamu da cutar damuwa wato “depression”.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *