Labarai

Emefiele ya yi alkawarin saka rubutun Larabci a sabbin takardun Naira – Lamido Sanusi

Spread the love

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Muhammadu Sanusi, ya ce magajinsa, Godwin Emefiele, ya yi alkawarin ajiye rubutun Larabci (Ajami) a kan sabbin takardun kudin Naira.

“An yi ta cece-kuce game da canjin wasu kudade na Naira. Na ji malamai daban-daban suna tsokaci, inda wasu ke nuna cewa za a cire Ajami a kan kudin Naira,” inji Mista Sanusi.

“Ina so in yi amfani da wannan kafar don tabbatar wa al’ummar musulmi bisa ga doka cewa babu irin wannan shirin. Tunda maganar ta taso mun zanta da wasu mutane a babban bankin, kuma sun tabbatar min da cewa babu irin wannan shiri.” Ya kara da cewa.

Tsohon Sarkin Kano ya bayyana haka ne a ranar Litinin, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

“Lokacin da wannan fahimta ta yadu, sai na yi magana da Gwamnan CBN da kansa, kuma ya tabbatar min da cewa babu wani shiri ko kadan na tsige Ajami.

“Don haka ina kira ga malaman addinin Musulunci da su daina aiki da rahotannin da ba su da tushe. Na san wasu malaman da ke yin wadannan tsokaci suna yin haka ne ba tare da binciken bayanan da aka kawo musu ba,” Mista Sanusi ya kara da cewa.

Sanarwar ta Mista Sanusi na zuwa ne a daidai lokacin da babban bankin ke shirin sake fasalin wasu takardun kudi na Naira.

A makon da ya gabata ne Mista Emefiele ya sanar da matakin sauya zababbun takardun kudi na Naira, bayan da “ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake fasalin kasa, samarwa da kuma rarraba sabbin takardun kudi a kan N100, N200, N500, da N1,000.”

Mista Emefiele ya ce daya daga cikin dalilan janye takardun da ake da su a yanzu shi ne don dakile ‘yan fashin da ke da dabi’ar karbar makudan kudade a matsayin kudin fansa.

Ya ce sama da kashi 80 cikin 100 na kudaden da suke zagawa ba su cikin rumbun bankuna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button