Fadar shugaban kasa ta tabbatar da yunkurin fashi da makami a gidan shugaban ma’aikatan Buhari (Chief of staff) Ibrahim Gambari

Fadar shugaban kasa a daren Litinin ta tabbatar da afkuwar fashi da makami a gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.
Lamarin, wanda aka ce ya faru a daren Lahadi ne a inda Garba Shehu ya bayyana shi da “wani yunkurin wauta”, an kuma ce basu yi nasara ba. 

 Binciken ya gano cewa mazaunin yana cikin yankin fadar shugaban kasa.  Wannan shine ‘yan mitoci kaɗan daga masaukin Shugaban ƙasar.

Garba Shehu bai bayyana ko an cafke wani daga cikin ‘yan fashin ba a lokacin hada wannan rahoton. Shehu, a cikin shafinsa na tweeter ya ce,
“Shugaban Ma’aikatan ya na sanarwa masu fatan alheri cewa babu wani abin damuwa.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *