Ferfesa Yakubu ya bayarda cin hancin Bilyan uku 3bn domin a koma dashi Karo na biyu

binciken da SaharaReporters ta yi ya nuna cewa samun wa’adi na biyu a ofis ba shi da sauki ga Farfesa Yakubu saboda dole ne ya raba makuddan kudade don saukaka nadin nasa.

A cewar wani babban mai fashin baki, Yakubu ya biya aƙalla N3bn cin hanci don a ƙara wa’adinsa na Shugaban INEC da wasu shekaru biyar.

“Ya biya N2bn gungun wasu dakarun Gwamnati karkashin jagorancin shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawan da kuma N1bn ga wani rukuni.

“Wadannan makudan kudaden an tura su ne kuma aka hada su da wani ma’aikacin gwamnati kuma darekta a hukumar ta INEC, wanda aka bayyana a matsayin mai kudin kuma mai kula da sashen dabaru.

“Har ila yau wani dan kwangila na hukumar, Mohammed Sani Musa ne ya taimaka wa daraktan, wanda a yanzu haka dan majalisar dattijai ne daga Jihar Neja da ke da alhakin buga katin zaben na INEC da aka yi amfani da shi wajen gudanar da zabe a karkashin wani kamfani (Activate Technologies),” majiyar ta shaida wa SaharaReporters .

An tattaro cewa sake nada Yakubu a matsayin shugaban INEC din ya kara yiwuwa ne Bayan da mutuwar tsohon Shugaban Ma’aikatan Shugaba Buhari, Abba Kyari, da Alhaji Isa Funtua, da kuma bacewa daga hasken Mamman Daura, babban mamba a kungiyar amintattun kungiyar aminan shugaba Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.