Galadima ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin shimfida wani juyin juya hali.

Galadima ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin shimfida wani juyin juya hali.

A watan Oktoba, ‘yan kasar da dama sun fito kan tituna a duk fadin kasar na tsawon kwanaki 12 suna kira da a yiwa‘ yan sanda garambawul tare da rusa runduna ta musamman mai yaki da fashi da makami (SARS) na ‘yan sanda.

Tsohon abokin na Buhari ya ce gwamnatin “tana kokarin haifar da juyin juya hali ta hanyar cirewa, hana mutane damar su ba bisa cancanta ba
Ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ke da zuciya mai girma kuma zai dauki kowa da kowa Babu Banbanci

“Lokacin da #EndSARS ta fara, ba su san cewa ‘ya’yan bamu maza da mata na talakawan Nijeriya, waɗanda ba sa iya samun abincin da za su ci, na iya hanasu  barci ba Inji Galadima.

“Yanzu, ina da yara kusan bakwai da ke da digiri na biyu. Ina da likitocin kiwon lafiya, amma babu wani daga cikinsu da za a iya aiki (a cikin aikin gwamnati) saboda ba ni da kudin da zan bayar, ”in ji Galadima.
Hatta abokaina da ke cikin gwamnati suna guje ni saboda ba za su so a gan ni tare da su balle in nemi wata alfarma.

“Wani tagomashi daga gwamnatin da Buhari ya kafa, wanda na yi aiki fiye da kowane dan Adam, gami da shi kansa Buharin, don kawowa shi cikin ofis, ace Kuma  ba zan iya kawo ɗa ya bashi  aiki ba?”

Leave a Reply

Your email address will not be published.