Ganduje zai dauki mataki Kan Dr. Victor Mbarika Wanda ya bashi Farfesa na Bogi.

Gwamnatin Jihar Kano ta fara nazarin matakin da zata ɗauka akan Dr. Victor Mbarika mutumin da ake zargi ya bawa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje takardar shaidar zama Farfesa ta bogi.

Wannan magana ta fito ne daga bakin mai taimakawa gwamna na musamman a ɓangaren yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai a wata tattaunawa da akayi da shi cikin shirin “Mu leƙa mu gano” na Freedom Radio.

Menene ra’ayinku?

Leave a Reply

Your email address will not be published.