
Gwamnatin Kano za ta kashe Naira biliyan 137 domin samar da ruwan sha a Gaya don magance kwalara da magance sauran kalubale, in ji Kwamishinan Yada Labarai, Muhammed Garba.
An cimma wannan matsayar ne a taron majalisar zartarwa ta jihar, in ji Garba a cikin wata sanarwa yau ranar Lahadi.
Mista Garba ya ce za a kashe kudin ne wajen gyaran shirin ruwa a yankin Wudil da garin Gaya da kewayenta; gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda shida da rijiyoyin burtsatse na hannu guda 30.