Garin Igbo-Ora shi ne babban birnin ƴan biyu na duniya

Shin ko kun san babban birnin tagwaye (ƴan biyu) na duniya?

Ƙabilar Yoruba ita ce wacce tafi yawan adadin ƴan biyu (tagwaye) a faɗin duniya.

Garin Igbo-Ora da ke jihar Oyo wanda ake yi masa laƙabi da babban birnin ƴan biyu na duniya shine yafi kowanne gari yawan adadin tagwaye a faɗin duniya domin da wuya ka je gida guda ɗaya baka samu tagwaye ba , sannan a duk haihuwa 1000 da za’ayi a garin ana samun adadin tagwayen da suka kai 158 a ciki.

Kamar yadda wani Bature ɗan ƙasar Burtaniya mai suna Patrick Nylander ya yi bincike a shekarar 1972 zuwa 1982

Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *