Labarai

Gobara ta kama gidan Sheikh Gumi a Kaduna.

Spread the love

Gobara da ta tashi a ranar Asabar ta kone wani bangare na gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, da ke Kaduna.

Ko da yake, ba a san musabbabin tashin gobarar ba, yayin da ake hada rahoton, wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce gobarar ta tashi ne a bangaren makarantar Islamiyya.

‘Mun ga hayaki yana fitowa daga ɗayan azuzuwan. Nan take muka ja hankalin jama’ar da ke wajen, muka fara diban ruwa don hana gobarar isa ga sauran gine-gine,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button