Labarai

Gobara ta kone kantuna a kasuwar Onitsha

Spread the love

Wasu shaguna a babbar kasuwar Ose, Onitsha, jihar Anambra, sun kone kurmus.

Har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, amma an tattaro cewa ta tashi ne da misalin karfe 1:02 na safiyar ranar Asabar.

Shagunan suna a lamba 4, titin Ajasa, inda ake sayar da ganguna na sinadarai.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra, Martin Agbili ya fitar, ya ce jami’an kashe gobara da aka tura wurin da lamarin ya faru nan take, bayan da suka yi ta kiraye-kirayen sun yi artabu da gobarar duk cikin dare.

Ya ce, “da misalin karfe 1:02 na safiyar ranar Asabar ne hukumar kashe gobara ta jihar Anambra ta samu kiran tashin gobara a lamba 4 titin Ajasa, babbar kasuwar Ose, Onitsha, inda suke sayar da ganguna na sinadarai.

“Nan da nan, mun tura motar kashe gobara da jami’an kashe gobara wadanda ba su da tsoro zuwa wurin da gobarar ta tashi. Muka yi gaggawar shiga aiki, mun yi yaƙi da gobarar, muka sarrafa kuma muka yi yaƙi da ita har ta tsaya.

“Ba a san musabbabin tashin gobarar ba saboda babu kowa a wurin lokacin da ta tashi. Ko da yake gobarar ta lalata kusan shaguna uku amma ba a samu asarar rai ba yayin da gobarar ta tashi. An ceto da yawa yayin da muka hana gobarar bazuwa zuwa wasu shaguna da ke kusa da wurin da gobarar ta tashi.

“Yana da mahimmanci a san cewa dole ne a koyaushe mu kashe kayan aikin mu na lantarki da musamman lokacin da ba a amfani da su.

“A guji duk wani abu da zai iya haifar da barkewar gobara a wannan kakar.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button