Labarai

Gobara ta kone shaguna 150 a kasuwar Kachako da ke Kano

Spread the love

Gobara ta kone wasu shaguna 150 a babbar kasuwar Kachako da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano.

Wannan labarin gobarar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya fitar a Kano.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin.

“Mun samu kiran gaggawa a tashar kashe gobara ta Takai da misalin karfe 01:13 na rana. daga sashin tsaro na karamar hukumar kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 01:21 na rana domin hana gobarar bazuwa zuwa sauran shaguna.

“Girman wuraren kasuwa yana da kusan ƙafa 2,000 da ƙafa 1,500 da ake amfani da shi azaman babbar kasuwa.

“Mun yi nasarar ceto kusan matsugunai 800 daga gobarar,” in ji sanarwar.

Ya ce ana zargin masu shan taba ne suka tayar da gobarar saboda ranar ta kasance ranar kasuwa.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button