Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka

Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne ‘yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

A ranar Laraban kafin a sako daliban, iyayensu sun yi zanga-zanga a gaban majalsar dattawa domin bukatar a sakar musu ‘ya’yansu.

A yayin zantawa da wani gidan talabijin, daya daga cikin iyayen daliban ta zargi Gumi da kaisu wurin wani bafulatani mai suna Ahmed wanda ya karba N800,000 a hannunsu.

“Muna ta zuwa taro, An kaimu gidan Gumi wanda yace mu samu wani Ahmed. Na manta sunanshi,” tace.

An gayyaci wani bafulatani kuma mun hada N800,000 amma yace kudin kaiwa da kawowa ne.

Na yi kuka inda nace mishi bani da miji kuma ni kadai nake kula da yarana, amma sai yace hakan bai dame shi ba.”

Amma Gumi ya sanar da TheCable cewa wannan zargin “rashin hankali ne” yayin da aka tuntubeshi a ranar Laraba. Malamin wanda aka san yana iya tunkarar ‘yan bindigan, yace bai san da wannan cinikayya ba.

“Wannan rashin hankali ne. Ban san komai a kan wata cinikayya ta kudi ba,” yayi martani a sakon kar ta kwana.

Daga Ahmad Aminun Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *