Gwamnatin Jahar Kano Ta Saki Sakamakon Jarrabawar (qualifying), Za Kuma Ta Biyawa Dalibai 29,125 Kudin Jarrabawar NECO.

Ma’aikatar ilimi ta jahar Kano ta saki sakamakon jarrabawar (qualifying) da yan Aji 2 na babbar sakandire da sukeyi domin zabo daliban da za’a biyawa jarrabawar ‘karshe ta sakandire.

Gwamnatin jihar Kano ta amince da sakin sakamakon jarrabawar ne biyo bayan gabatarwar da Kwamishinan Ilimi na jihar Kano Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya gabatar wa Majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Kwamishinan ya nuna godiyarsa ga gwamnan Jihar da dukkanin membobin majalisar kan wannan yardar.

Gwamnatin Jiha za ta tallafawa dalibai da kudaden rajista Su 29,126 waɗanda suka sami shaidar cin jarrabawar (qualifying) da suka haɗa da darasin Lissafi dana Turanci inda za’a kashe zunzurutun ‘kudi N489,258,000 Don yiwa dalibai rijistar jarrabawar NECO.

Yayin da yake taya murna ga daliban da suka samu nasara Kwamishinan ya bukace su da su maido da martabar gwamnatin ta hanyar tabbatar da cewa sun sun cinye jarrabawar su ta NECO da NBAIS da gwabnatin zata biyamusu.

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.