Gwamna A.A Sule na nasarawa yayima Buhari takwara da tagwayen da aka Haifa masa.

Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa ya bayyana dalilin da ya sa ya sanyawa tagwayen ‘Ya ‘yansa sunayen Shugaba Muhammadu Buhari da Sanata Umar Tanko Al-Makura.

Gwamnan ya ce ya yanke shawarar sanya wa ‘ya’yansa sunan Buhari da Al-Makura ne bisa la’akari da girmamawar da yake yi wa shugabannin biyu.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen bikin sanya sunan tagwayen da matarsa ta biyu, Hajiya Farida Abdullahi Sule ta Haifa masa.

An gudanar da bikin ne a Fadar mahaifin Gwamna, Sarkin Gude a karamar hukumar Akwanga, Alhaji Sule Bawa.
“Na sanya musu sunan Shugaba Muhammadu Buhari da Sanata Umar Tanko Al-Makura saboda karramawa da girmamawar da nake yi wa shugabannin biyu.

“Na yi alƙawarin ci gaba da fafutukar neman ingantaccen ilimi ga ɗaukacin yara a jihar,” in ji shi.

Taron ya samu halartar musamman, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dr Emmanuel Akabe, Sen. Abdullahi Adamu, da Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Alh. Ibrahim Balarabe Abdullahi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.