Labarai

Gwamna Bello ya ayyana dokar hana fita a Neja bayan kashe wani basarake

Spread the love

Takaddamar dai ita ce ta taimakawa jami’an tsaro domin daidaita al’amura a yankin, da wasu dalilai, inji gwamnatin.

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya kafa dokar hana fita a garin Lambata dake karamar hukumar Gurara ta jihar, biyo bayan wani kazamin fada da yayi sanadiyar mutuwar hakimin Lambata Mohammed Abdulsafur.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in yada labarai na ofishin SSG, Lawal Tanko ya fitar.

Matane ya kara da cewa gwamnan ya bada umarnin a sanya dokar hana fita a garin na Lambata daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe daga ranar Lahadi 15 ga watan Janairu, 2023 har zuwa wani lokaci.

SSG ta bayyana cewa an sanya dokar ne domin a taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankin, da ceton rayuka, da kuma ba da damar maido da doka da oda.

A cewarsa, “Gwamnati ta yi Allah wadai da ta’addanci da rashin bin doka da oda da aka samu a garin Lambata.”

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna yankin da su baiwa jami’an tsaro hadin kai a aikin gaggawa na maido da zaman lafiya a garin Lambata, yayin da ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button