Labarai

Gwamna Lolo Na Niger yasa Jami’an DSS sun kama matashi domin yayi rubutu a Facebook kan yadda gwamnan ya gaza gyara asibitin da aka haife shi na Garin Rijau.

Spread the love

Rahoton Dake Zuwa mana na cewa Jami’an tsaron farin kaya DSS sun kama wani matashi Shamsudden Mohammed Hakimi sun kulleshi na tsawon kwanaki takwas bisa umarnin Gwamnan jihar  Niger Abubakar Sani Bello Lolo.

matashin Dan asalin Garin Rijau yayi wani rubutu ne a shafinsa na Facebook Yana Mai kalubalantar gwamnan jihar da Gaza gyara asibitin Garin Rijau wanda Kuma a acikin asibitin ne aka haifi gwamnan kamar yadda matashin ya rubuta a shafin nasa wannan al’amari yasa gwamna Bello ya bawa DSS umarnin kamawa da tsare matashi na tsawon kwanaki takwas yanzu haka kamar yadda Dan uwan matashin ya sanar mana.

A zantawar da Mikiya tayi da mukhtar Hakimi wanda Dan uwa ne ga Shamsudden Mohammed Hakimi Dake tsare a hannun Jami’an na tsaro Yana Mai cewa Haryanzu Dan uwanmu Yana hannun Jami’an tsaron DSS Kuma Jami’an tsaron sun tabbatar da cewa gwamna ne ya basu umarnin kamashi Kuma gwamnan yayi tafiya Zuwa Kasar Morocco yace sai ya dawo zai yi maganar yadda za’ayi da matashin.

Mukhtar Hakimi yace Dan uwan nasa bashi da lafiya Yana fama da wani ciwo Mai tsanani da yake tashi lokaci lokaci.

Zuwa yanzu munyi kokarin Jin ta bakin wani jami’in gwamnatin jihar Amma al’amarin garaga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button