Labarai

Gwamna Yahaya bello Yana son zama Shugaban kasar Nageriya ne domin kare darajar Matasa.

Spread the love

A lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan Jaridu Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Kogi, Jamiu Asuku ya yi kira ga matasan Nijeriya da su marawa Gwamna Yahaya Bello baya ya zama shugaban Nijeriya a 2023.

Asuku ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Gombe a taron da ƙungiyar “Rescue Nigeria Mission” (RENMISS) reshen Arewa maso Gabas – wata ƙungiyar tallafawa matasa masu fafutukar ganin an samar da kyakkyawar shugabanci da matasa, ta shirya domin yin ƙira ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya tsaya takaran shugaban ƙasa a zaben 2023.

Asuku ya ce dole matasa su fara dubawa tare da goyon bayan ɗan uwan su matashi domin samun matsayi a babban matsayi a siyasa a Zaɓe mai zuwa.

Shugaban ma’aikatan ya ce akwai buƙatar matasa su yi gangamin neman takarar shugaban ƙasa na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya na mai cewa shi ne zai iya gyara ƙasar nan yadda ya kamata.

Ya ce, “Gwamna Yahaya Bello ne kaɗai zai samar da ingantaccen shugabanci da shugabanci nagari idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaben 2023.

Shugaban ma’aikatan, duk da cewa shi ne ya wakilci gwamnan, ya ce shugabancin Bello shine wanda zai amfani matasa matuƙa.

Ya ce burin gwamnan na matasa ne da suka shirya ganin ci kafa gaban kasa.

Ya kuma jaddada cewa, gwamnan ya karya lagon kabilanci a jihar sa, kuma ya nuna kansa a matsayin cikakken mai kishin Najeriya a naɗe-naɗe muƙaman siyasa da ya yi wa ƙabilu daban-daban, tare da bajintar da ya nuna wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar Kogi.

Kodinetan kungiyar na ƙasa A.S Damat, wanda ya jagoranci sauran shuwagabannin matasa a faɗin Arewa maso Gabas a nasa jawabin ya yaba wa Gwamnan bisa gagarumin nasarorin da ya samu ta fuskar samar da ababen more rayuwa, tsaro, ilimi, haɗa kan mata da matasa da dai sauransu.

Sun amince da Gwamna Yahaya Bello a matsayin ɗan takara ɗaya tilo da ya dace kuma zai iya jagorantar Najeriya daga dimbin kalubalen da ta ke fuskanta.

Mai baiwa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin matasa da dalibai, Comr. Ahmadu Jibril wanda ya gabatar da jawabin buɗe taron ya bayyana nasarorin da Gwamnan ya samu, tun daga samar da ababen more rayuwa zuwa kiwon lafiya, ƙarfafa matasa da mata, ilimi, tsaro da galibin yadda ya shawo kan rikicin COVID-19 da ya durkusar da tattalin arziƙin duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button