Labarai

Gwamna Zulum ya bayyana talauci a matsayin babban musabbabin rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Juma’a, ya bayyana talauci a matsayin musabbabin rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

Zulum, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da ‘ya’yan kungiyar Tsofaffin Yaran Barewa (BOBA) a gidan gwamnati da ke Maiduguri, ya jaddada cewa akwai alaka kai tsaye tsakanin talauci, aikata laifuka, da kuma tada kayar baya.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a ranar 17 ga watan Nuwamba ta ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci.

Sai dai Zulum ya ce shugabanci nagari maganin rikicin Boko Haram ne.

Dubun dubatar mutane ne aka kashe yayin da wasu sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu a rikicin Boko Haram da ya fara a jihar Borno a shekarar 2009.

Gwamnan ya ce: “A gare mu shugabanni, akwai bukatar mu yi abin da ake bukata, mu samar da yanayin da mutane za su iya samun hanyar rayuwarsu. Dangantaka tsakanin zaman lafiya, tsaro, da ci gaba, bai kamata a wuce gona da iri ba, idan babu zaman lafiya, babu ci gaba.

“Kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya bayyana karara cewa tsaro yana karkashin gwamnatin tarayya ne amma hakan baya nufin gwamnatocin jihohin ba su da wani muhimmanci, sai dai kuma sun taka rawar gani a halin da ake ciki a jihar.

“Da zarar babu shugabanci nagari, babu abin da za a iya samu. A matsayinmu na shugabanni, muna bukatar mu tabbatar da ladabtarwa da rikon amana sannan samar da duk wani sa ido da tantancewa.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button