Labarai

Gwamnan jihar Anambra ya yi karin albashin ma’aikatan jihar da kashi 10%

Spread the love

Soludo ya sanar da karin albashin ma’aikatan Anambra da kashi 10%.

.

Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya sanar da karin albashin ma’aikatan jihar da kashi 10% daga watan Janairun 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ma’aikatan gwamnati ta shekarar 2022 a dakin taro na Jerome Udoji State Secretariat Complex, Awka.

Ya kuma sanar da kyautar N15,000 na Kirsimeti a fadin hukumar domin baiwa ma’aikata damar siyan kayan abinci ga iyalansu.

A fannoni biyar na abubuwan da gwamnatin Soludo ta samar, ya ci gaba da cewa jihar ba za ta taba zama a hannun miyagu ba domin yana fatattakar su tare da wargaza ayyukansu da suka hada da zaman dirshan da ke gurgunta ayyukan gwamnati da tattalin arzikin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button