Gwamnan jihar Imo ya sallami kwamishinoni 20

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya kori Kwamishinoninsa 20

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya yi tankade da rairaye wa majalisar gwamnatinsa inda ya yi waje rod da kwamishinoni ashirin.

Wannan shine garambawul mafi girma da ya yi tun bayan shigowarsa ofis a shekarar da ta gabata.

Gwamna Uzodinma ya fatattaki kwamishinonin yayin da dukkanin su suke ofishin su suna more rayuwar a tsakar ranar yau Laraba.

Cikin kwamishinoni takwas da ya kora akwai Kwamishinan ayyuka da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Kwamishinan kiwon lafiya da Kwamishinan Kuɗi.

Sauran sun hada da Kwamishinan harkokin mata da yawon shakatawa, sai Kwamishinan matasa da wasanni da kuma Kwamishinan Fasahar Zamani.

Idan za a iya tunawa makonni biyu da suka gabata gwamnan ya yi zargin cewa akwai wasu daga cikin kwamishinonin nasa dake yi wa gwamnatinsa kafar Ungulu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *