Gwamnati ta gaza ace sai talaka ya biya haraji za’a Shiga Gona ~Atiku

Ya isa zama abin takaici mutuka da tada hankali ga duk ‘yan kasa, saboda taazzar matsalar tsaro a Najeriya.

Yanzu al’amarin ya kai ace bata gari na yadda suka ga dama da rayuwar mutane tare da cin karen su ba babbaka.

Hakika labarin da nake samu game da al’umar
Dan Kurmi a karamar Hukumar Maru dake Jihar Zamfara abin takaici ne, saboda yadda Yan ta’adda ke sanya musu haraji kafin su shiga gonakin su, wannan ba abin amincewa bane.

Wani abin takaici shi ne na sami labarin sun biya ‘Yan ta’addar Naira Dubu Dari Takwas (N800,000) amma sun hana su shiga gonakin domin daukar amfanin gonar su. Kuma haka abin yake ga al’ummar yankunan Duhuwa Saulawa, Mai Kulungu, Baudi da Zagadi.

Wannan ya nuna gazawa a fili, ya kamata Gwamnati da jami’an tsaro su tashi tsaye, wajen daukar matakan da Jama’a zasu zauna a garuruwan su cikin aminci, su kuma al’umma na da gudummawar da zasu bayar ta hanyar sanar da jamian tsaro bayanan duk wani motsi da basu yarda da shi ba.

Lokaci ya wuce da shugabani zasu rika tura laifi kan wasu, lokaci ya yi da shugabani zasu rage yawan zance su yawaita daukar matakai.

A karshe ina addua da fatan Allah ya kawo karshen wadannan masifu na rashin tsaro da zaman lafiya a Arewa da Najeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.