Gwamnatin Buhari ta fara Horas da mutu 17,000 sana’ar kiwon Zomo.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirye-shiryenta na sanya matasa dubu 17, 000 yin noman zomo, domin bunkasa kiwon zomaye a kasar Najeriya.

Sakataren zartarwa na Hukumar Raya Kasa ta Noma (NALDA), Paul Ikonne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa hukumar ta tsara aikin ne domin jawo hankalin matasa a Kudancin kasar kan kiwon zomo.

Ya ce, wadanda za su ci gajiyar ba za a horar da su ba ne kawai, a’a za a karantar da su ne kan yadda za su girbe fitsarin da kashin zomaye (don takin zamani), daga inda za su samu akalla N100,000 a kowane wata.

Ikonne ya bayyana cewa kashi na farko na shirin ya fara a jihohin Abia, Imo da Oyo, yana mai cewa manufar ita ce aiwatar da aikin a fadin jihohi 18.

“Tuni Shugaba Muhammadu Buhari, ya amince da shirin tare kuma da fitar da kudade don aiwatar da aikin, inji Sakataren.

Ya shawarci masu niyyar su amfana, da su ziyarci ofisoshin NALDA a cikin jihohinsu ko kuma su shiga shafin yanar gizon gizon www.nalda.ng don samun bayanan da ake bukata game da kiwon zomo.

Ikonne ya kara da cewa a karshen wata, za’a biya matasa kudi bisa ga yawan fitsari da kashin zomaye da suka iya tarawa.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *