Labarai

Gwamnatin Buhari ta yi amfani da Naira Biliyan 120 da ta kwato daga hannun barayi wajen gina tituna da gadoji – Lai Muhammed

Spread the love

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Muhammed, ya yi ikirarin cewa an ware kudaden da suka kai Naira biliyan 120 da aka kwato ta hanyar dokar hana laifuka (POCA) 2022 don gina manyan hanyoyi da gadoji da gwamnatin Buhari ke jagoranta.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin bugu 8 na katin zabe na shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja ranar Laraba.

A watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin dokar hana fasa-kwauri (Madogara da Sarrafawa), da kudirin halasta kudaden haram, na shekarar 2022 da kuma dokar ta’addanci (Rigaka da Hana) da zai zama doka don inganta yaki da safarar kudade a kasar nan da tsarin ba da tallafin ‘yan ta’adda.

Shugaban ya ce amincewa da kudirin ya yi daidai da alkawurran da gwamnatinsa ta dauka na kawo karshen ta’addanci da sauran ayyukan rashawa a kasarnan.

Ministan a wajen taron ya yi ikirarin yakin da gwamnatin Buhari ke yi da cin hanci da rashawa abin yabawa ne ta hanyar sanya hannu kan wadannan muhimman kudirorin doka.

Ministan ya ce: “A bisa sabuwar dokar, a yanzu duk hukumomin gwamnati da abin ya shafa sun bude ‘Confiscated and Forfeiture Properties Account’ a babban bankin Najeriya.

Mohammed ya kara da cewa, “ana amfani da kudin ne wajen kammala ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasar nan kamar gadar Neja ta biyu da kuma manyan hanyoyin Legas-Ibadan da Abuja-Kano”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button