Gwamnatin Jihar Filato ta gano wani ma’aikacin Gwamnati mai karbar Albashin mutane dari takwas 800 shi kadai.

Gwamnatin jihar Filato da ke yankin tsakiyar Najeriya ta kori ma’aikata fiye da 500, ciki harda Wani ma,aikaci mai karbar albashin mutane dari dakwas 800 bayan da aka gano cewa sun yi amfani da takardun bogi, da kuma rage shekarunsu na haihuwa yayin gabatowar lokacin barin aiki.

Hakan ya sa aka kafa wani kwamiti na musamman, domin kara tantance ma’aikatan jihar da sauraren ƙorafe-ƙorafensu.

A can baya dai wani bincike da gwamnatin jihar ta gudanar ya bankado ma’aikatan bogi, ciki har da wani mutum guda da ke karbar albashin ma’aikata fiye da 800 shi kadai a jihar.

Mista Dan Manjang, kwamishinan yada labarai na jihar shine yafitar da sanarwar.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *