Gwamnatin jihar kaduna tayi fatali da sunayen jerin masu neman sarautar Zazzau

Gwamnatin Kaduna ta yi watsi da sunayen da masu zaben sabon sarki suka mika mata bayan ta gano an tafka maguni a lokacin zaben ta hanyar dankara wa masu zaben sarkin damman kudi domin su zabi ra’ayin wasu. daga majiyarmu ta Premium times sunce

Idan ba a manta ba mazu zaben sarki su biyar sun aika da takarda kunshe da sunayen ‘ya’yan sarki uku da suka zaba.

A wannan sunaye da suka aika masu zaben sabon sarki sun yakice sunan Ahmed Bamalli da gidan Sarautar Mallawa kwata-kwata inda suka raba kuri’un su ga mutum uku kacal.

A bisa wannan dalili ne, gwamnati ta sake bude kofa kowa ya nemi sarautar kuma wanda ya dace za a ba.

Karbar cin hanci

Majiya ta shaida mana cewa gwamnatin Kaduna ta gano cewa an baiwa masu zaben sabon sarki toshiyar baki da cin hanci, da hakan yasa ba zata yi amfani da sunayin da suka mika mata ba.

Sannan kuma wadanda aka rabawa kudin kuma suka karba sun tabbatar wa gwamnati da bakunan su cewa tabbas an basu kudi kuma sun karba domin su zabi wani dantakara.

“ Kudade ne masu yawa kuma gwamnati ta gano yadda aka raba su da asusun bankunan da aka saka su. A dalilin haka karara ya nuna cewa an tafka magudi a wannan zabe da ka yi ta hanyar toshiyar baki da aka rabawa na kudade masu yawan gaske.

A dalilin haka gwamnatin Kaduna ta bude kofar duk mai so ya nema, kuma tuni ta ana aiki akan sunayen mutum 11 da ke neman kujerar sarautar Zazzau din.

Kakakin gwamnan Kaduna Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa har yanzu bai samu wani bayani gane da wannan bincike da muka yi ba, saidai yace gwamna El-rufai zai yi abinda ya dace a matsayin san a gwamna mai adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.