Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa Naira Marley shiga jihar

Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa mawaki Azeez Adeshina Fashola wanda a kafi sani da Naira Marley shigowa jihar domin gudanar da wani gangamin bikin ganawa da masoya.

Tuni sanarwa ta kararaɗe kafafen sadarwa na zamani akan zuwan Naira Marley jihar Kano a ranar Asabar 22 ga watan Mayu.

Sai Shugaban hukumar kula da yawon bude ido da gidajen bukukuwa, Yusif Ibrahim Lajawa ya gargadi gidajen shirya taro ko bukukuwa da shakatawa da akan su nesanta kansu daga karbar bakwancin Mawakin ko kuma su fuskanci fushin gwamnati tare da gurfana a gaban Kotu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *