Gwamnatin jihar Kano zata koma da Gidan Zoo Tiga

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ba da umarnin sauya Gandun namun dajin Kano daga inda yake yanzu a cikin garin.

Kwamishanan al’adu da yawon bude ido na jihar, Ibrahim Ahmed ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce wurin da yake a yanzu na wahalar da dabbobi wanda a cewarsa, ba sa son hayaniya.
Da yake magana da Freedom Radio, kwamishanan ya ce za a mayar da gidan zoo zuwa garin Tiga da ke karamar hukumar Bebeji ta jihar. Ya ce: “Muna aiki don sake komawa gidan ajiye namun daji na Kano saboda wurin da ake da gidan dajin yanzu yana kewaye da mutane. Yawancin waɗannan dabbobin ba sa son hayaniya. ”

“Saboda haka, za mu sake matsar da gidan ajiye namun dajin mu inganta shi zuwa matsayin na duniya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.