Labarai

Gwamnatin Jihar Kogi ta aminta zata biya Mafi karancin Albashin ma’aikata kan naira dubu talatin N30,000.

Spread the love

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Talata ya amince da tsarin biyan sabon mafi karancin albashi kan N30,000 ga ma’aikatan jihar.

Sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Arike-Ayoade, ta bayyana hakan bayan wani gagarumin taro da kungiyar kwadago a Lokoja.

Arike-Ayoade ta bayyana cewa jinkirin aiwatar da sabon Shirin biyan albashin ya faru ne saboda gazawar kwamitin da aka kafa na gudanar da taro akai-akai musamman sakamakon cutar ta COVID-19.

Sai dai Arike ta yabawa kungiyoyin da suka shirya domin fahimtar juna da hakurin da suka nuna ya zuwa yanzu, wanda hakan ya sa aka amince da aiwatar da tsarin yanzu.

Shima da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Cif Edward Onoja, cike da yabo da jinjina ga kungiyar kwadagon bisa jajircewar da suka yi wajen cimma yarjejeniyar cikin ruwan sanyi, ba tare da daukar matakin yajin aiki ba.

“Gwamna Yahaya Bello yana da kishi da son jin dadin ma’aikatan gwamnati kuma zai ci gaba da baiwa ma’aikatansa fifiko, inji Onoja.

Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar, Misis Hannah Odiyo, ta ce, “Da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sabon tsarin na mafi karancin albashin ma’aikata na kasa, kwamitin ya kammala aikinsa cikin lumana, ba tare da yajin aikin ba.

Da yake mayar da martani, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Mista Onuh Edoka, ya yabawa Bello “saboda daukar sa da wannan mataki wajen sanya hannu kan sabon mafi karancin albashi.

“An dakatar da yajin aikin tun farko ga gwamnatin jihar bisa la’akari da wannan gagarumin yunkuri da gwamnati ta dauka.

“Hakika muna yabawa gwamnatin jihar bisa sanya hannu kan yarjejeniyar tare da aiwatar da aikin nan take na baiwa ma’aikatan jihar wani sabon salo na rayuwa.

“Saboda haka, muna tabbatar muku da jajircewar ma’aikatan gwamnati na samar da ingantaccen aiki a dukkan bangarorin tattalin arziki,” in ji shugaban.

Yarjejeniyar ta kuma shafi ma’aikatan jihar da ma ma’aikatan kananan hukumomi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button