Gwamnatin Jihar Neja Ta Kori Ma’aikatan Gwamnati Saboda Rashawa.

A jiya alhamis ne dai gwamnatin Jihar Neja ta kori ma’aikatan gwamnati 80 bisa zargin sanya kansu a kan albashi sama da yadda suke a yanzu.

Shugaban ma’aikatan jihar, Salamatu Abubakar, wanda ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai yau a Minna, ta ce majalisar zartarwar jihar ce ta amince da korar tasu a zaman da ta yi a yau Alhamis.

Shugabar Ma’aikatar, Abubakar ta kara da cewa jami’an sun sanya kansu a kan alawus sama da matsayin da suke da shi a yanzu.

Ta ce an gabatar da rahoton kwamitin ga ofishin shugaban ma’aikatan wanda ya mika shi ga babban Odita don daukar mataki.

Shugaban ma’aikatan ta kara da cewa daga baya an gabatar da rahoton ga majalisar zartarwa ta jihar, wacce ta amince da korar jami’an 80 daga aiki a yau Alhamis.

Ta ce jami’an sun kasance daga Ma’aikatun Lafiya da Ilimi, da kuma Ma’aikatan Kula da Asibitoci da Hukumar Gudanarwa da Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Pramary health.

Sauran sun hada da Makarantar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tunga Magajiya, Makarantar ungozoma ta minna, Babbar Kotun da kuma na Kotun Shari’a ta bangaren shari’a Jihar.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.