Gwamnatin katsina ta Karyata Gwamnatin tarayya Kan Batun Sako dalibai 333 na Yan Makaranta.

A Rahotan da muka samu yanzu Kan Sakin daliban 333 Gwamnatin jihar katsina ta Karyata Batun BBC ta yi magana da Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa da misalin ƙarfe 3:15 agogon Najeriya inda ya ce batun cewa an sako su ba gasikiya bane, amma ana sa ran cewa za a sako yaran ba da daɗewa ba.

Tun da farko kafar watsa labarai ta Arise TV ce ta sanar da ceto yaran, inda daga baya ita ma mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin waje da ‘yan Najeriya mazauna ƙetare, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ce an sako yara 333.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *