Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta na kawar da talauci da rashin aikin yi a ƙasar

A shirye muke mu kawar da Talauci da Rashin Rashin Aiki

Gwamnatin Tarayya ta jaddada kudirin ta na magance talauci tare da magance rashin aikin yi a ƙasar, inda tace shirye-shiryen data ɓullo dasu, sun taimaka wajen samun nasara.

Gwamnatin tace yawaitar samun yara marasa zuwa makaranta da aka samu a shekarun da suka gabata, a yanzu sun ragu, sakamakon shirye-shiryen data bullo dasu, daga cikin su akwai shirin ciyar da ɗalibai ƴan makaranta.

Hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin ta kara wa’adin kwamitin dake kula da shirin ciyarwa, tare da yin kira a garesu dasu bayar da gagarumar gudunmuwa domin magance matsalolin kasar nan.

Ministar jin ƙai da walwala Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka a lokacin da take jawabi a Abuja, a ranar Laraba, inda tace kaddamar da Shuwagabannin zai taimaka wajen cigaba da bayar da goyon baya domin samun cigaba.

Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka, a tabakin wakilin ta Kuma Shugaban shirin saka hannun jari na Kasa Dr Umar Bindir, inda yace Gwamnati na bakin kokarin ta domin magance Talauci tare da samar da ayyukan yi.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *