Labarai

Gwamnatin Najeriya za ta fara mataki na biyu akan wadanda ake zargi da Boko Haram

Spread the love

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami (SAN), ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da shari’ar wadanda ake zargi da ta’addancin Boko Haram da ake tsare da su a sassan soja daban-daban a Najeriya.

Malami wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata yayin zaman kotu na musamman na sabuwar shekarar shari’a ta 2022/2023 na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kudaden da za a gurfanar da wadanda ake tuhuma gaba daya.

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin in yaba da mataki na musamman da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a baya-bayan nan na samar da kudade da sauran kayan aiki domin fara shari’ar kashi na biyu na wadanda ake zargi da Boko Haram,” Malami wanda ya samu wakilcin lauyan gwamnatin tarayya kuma babban sakatare na ma’aikatar shari’a ta tarayya, Beatrice Jedy-Agba, ita ce ta bayyana haka.

“Shawarata ce cewa sabbin sabbin hanyoyin da aka bullo da su a cikin al’amuran zabe suma a fadada su zuwa wasu lokuta wadanda ke da matukar muhimmanci a fannin tattalin arziki ko kasuwanci, la’akari da illolin jinkiri wajen kawo karshen irin wadannan shari’o’in.” Ya kara da cewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button