Labarai

Gwamnatin Shugaba Buhari ta magance matsalar tsaro a Nageriya idan muka Auna da Shekara ta 2015 ~Cewar Gwamna Yahaya Bello.

Spread the love

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta magance matsalar rashin tsaro, yana mai cewa an shawo kan kalubalen da aka fuskanta a shekarar 2015.

Bello ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’ a wani shiri da ake gabatarwa a duk Ranar litinin inda ya kara da cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen cika alkawuran zaben da ta yi wa ‘yan Najeriya.

Ya kuma yabawa gwamnatin APC bisa inganta kayan aikin jami’an tsaro tare da kula da jin dadin ma’aikata.

“A kan tsaro, an magance kalubalen da ake fuskanta a lokacin. Muna fuskantar kalubale ba kawai a Najeriya ba har ma a duk fadin duniya,” inji shi.

“Idan aka kwatanta shi da halin da ake ciki kafin babban zaben 2015, bambamcin ya fito karara. Akwai wasu abubuwa da dama da ake yi don hana wannan rashin tsaro da ba za a taba kawowa kafafen yada labarai su tattauna ba.

“Wannan shine karo na farko da muke da Shugaban kasa wanda zai iya siyan kayan aikin da ba a taɓa kasancewa an saya ba Wasu sun tsufa kuma wasu ba su wanzu kafin yau. “

Yayin da ya amince cewa akwai bukatar a ci gaba da samun nasara wajen tunkarar abin da ya bayyana a matsayin barazanar tsaro da ke kunno kai a kasar, Bello ya bayyana kwarin gwiwar cewa dakarun sojin na iya tunkarar lamarin.

Gwamnan na Kogi ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari bisa yadda ta inganta fiye da yadda ta kasance a shekarar 2015.

A bangaren tattalin arziki kuwa, Bello ya ce gwamnati mai ci ta yi kyau, ba tare da la’akari da wasu kalubale ba, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki.

Ya bayyana cewa ana yakin cin hanci da rashawa ne domin fallasa mutanen da suka wawure dukiyar kasa.

Bello ya kara da cewa, “Wace kasa ce ta wannan duniya? Har yanzu akwai sauran abubuwa da yawa da ya kamata a yi, na san hakan sosai.

“Wannan gwamnatin ce ta gwammace ta fallasa ‘yan cin hanci da rashawa a tsakaninmu Wanda A da, ba ka kuskura ka yi magana a kai.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button