Gwamnatin Shugaba Buhari tana bakin ƙoƙarinta wajan dawo da zaman lafiya a Najeriya-Lai Mohammed

Gwamnatin Buhari na bakin kokari wajen samar da zaman Lafiya a Najeriya- Lai Mohammed

Ministan yada Labaru da al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya baiwa ƴan Najeriya tabbacin cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, nayin bakin kokarin ta domin dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin Kasa.

Ministan ya bayyan haka, a lokacin da ya karbi Shuwagabannin Cibiyar Horas da Hulda da Jama’a, a wata ziyara da suka kai mashi a ofishin sa dake Abuja.

Jawabin shi na kunshene a cikin wata sanarwa da Mai Taimaka masa na musamman akan Kafafen Yada Labaru, Segun Adeyemi ya fitar.

Lai Mohammed ya jaddada cewa Gwamnati na bakin kokarin ta domin magance matsalar tsaro a kasa, a ta bakinsa tsaro na kawo cigaba a Kasa.

Ya kuma yi Kira da Shuwagabannin Cibiyar, da su bayar da gudunmuwa wajen tabbatar da cewa kasar ta samu zaman lafiya da tsaro.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *